Yaushe Za’a Fara Azumin Watan Ramadan Na 2024?

A ranar 11 ga watan Maris, 2024 ne ake sa ran za a fara azumin watan Ramadan a mafi yawan kasashen musulmi, a cewar wata sanarwa da cibiyar nazarin taurari ta duniya ta fitar.

Babban haɗin gwiwa tsakanin rana da wata zai faru ne a ranar 10 ga Maris da ƙarfe 9 na safe agogon GMT, a cewar binciken.

Sai dai sanarwar ta ce ganin jinjirin watan a ranar 10 ga watan Maris ba zai iya yiwu ba daga ko’ina a kasashen Larabawa da na Musulunci, ko da ido ko kuma ta hanyar amfani da na’urar hangen nesa.

Ana sa ran ganin watan zai fadi jim kadan bayan faduwar rana a garuruwan kasashen musulmi a ranar 10 ga watan Maris.

A Makka, ana hasashen wata zai fadi minti 13 bayan faduwar rana a lokacin da ya kai awa 6 da minti 22.

Hakazalika a birnin Alkahira na Masar, wata zai fadi minti 14 bayan faduwar rana a lokacin da ya cika awa 7 da minti 2.