Al'umma

Tarihin Sheikh Abubakar Gero Argungu

Sheikh Abubakar Gero Argungu, wanda shahararren malamin addinin Muslunci ne na kungiyar Izala, wato Jama’atu Izalatul Bid’a Wa’ikamatus-sunnah (JIBWS).

Kamar yanda mutane suka sani, ko suke ji ana kiran shi, (Abubakar Gero Argungu), garin Argungu wanda yake a cikin jihar Kebbi dake Arewacin Najeriya shine garin da malamin addinin musuluncin ya fito.

Sheikh Abubakar Gero Argungu

Sheikh Gero Argungu, sannannen malami wanda har yau yana yin wa’azi na addinin musulunci a ciki fa wajen Najeriya, musamman a ƙasashen Afrika irin su; Jamhuriyar Niger, Ghana, Kamaru, Chadi, Benin sauran wasu ƙasashen da mu iya ambatawa ba.

Har yau Sheikh Gero Argungu shi ne sakataren kungiyar na kasa a halin yanzu na daya daga cikin fitattun kungiyar addini a Najeriya, wacce muka ambata a samu wato IZALA.

Sheikh Gero a cikin kakin agaji ta ƙungiyar IZALA

Shugaban wannan kungiya na kasa wani fitaccen malamin addinin musulunci ne a Najeriya mai suna Sheikh Abdullahi Bala Lau.

Kungiyar addini ta yi suna sosai a yankin arewacin Najeriya. Makasudi da makasudin wannan kungiya shine kawai inganta addinin musulunci.