Philip Shaibu Ya Durƙusa A Gaban Oshiomhole Bayan Fita Daga PDP Zuwa APC
Mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu, ya koma jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a hukumance daga jam’iyyar PDP.
Mataimakin gwamnan ya samu rakiyar fitattun ‘yan jam’iyyar Legacy Group ta PDP karkashin jagorancin Dan Orbih a lokacin da yake komawa APC.
Shaibu ya taka kai tsaye inda tsohon gwamnan jihar, Sanata Adams Oshiomhole, ya zauna a wurin taron ya durkusa a gabansa, inda magoya bayan jam’iyyar suka jinjina ma sa.
Ya ce, “A madadin kungiyar Legacy, ina sanar da tafiyar mu zuwa jam’iyyar APC. Mun zo ne domin mu kara wa jam’iyyar daraja.
“Lokaci ya yi da za mu mayar da jiharmu. Ba za mu yi magana da yawa ba saboda aiki zai yi magana a gare mu. Ba ma tsoro. Mun shirya don ci gaba.
“Mu ‘yan gida a shirye muke mu mayar da jiharmu ta hannun dan takarar gwamna a jam’iyyar APC, Monday Okpebolo, da abokin takararsa, Dennis Idahosa.
“Mu ba masu tayar da hankali ba ne, amma idan ya zo, za mu yi amfani da shi don shafa jikin mu, kuma mu ci gaba.”