Lafiya

Magungunan Ciwon Sanyin Mata 10 Na Gargajiya

A yau zamu yiwa yan uwa mata bayani game da wasu magungunan sanyi na gargajiya da ya kamata masu irin wannan lalurar su gwada.

<•> Shan yoghurt wanda ba yi da sugar a cikin shi mai dauke da Lactic acid a ingredient ɗin sa, ki sha kuma in za ki kwanta ki ɗiba ki sanya a cikin al’aurar ki, ki kwana da shi yana kashe infection ta ciki da waje.

<•> Hulba yana mutukar kashe kwayoyin cuta da hana zuban ruwa, shan sa a ruwan zafi da zuma, ko ɗiban garin a haɗiye da ruwa ko yoghurt yana mutuƙar kashe kwayoyin cuta. Haka a jiƙa da ruwa na minti ko a dafa a rin ka tsarki ko zama da shi sau biyu a rana yana kashe cututtukan sanyi.

<•> Tafarnuwa shugaba kuma tana daga cikin manya maganin cututtuka, in kina hada magungunan sanyi kuma baki amfani da tafarnuwa za ki sha wuya. Ki rin ƙa haɗiyan tafarnuwa ko da kwaya 1 ne idan kin tashi da safe, ko ki rin haɗiya tare da yoghurt ɗin da na yi bayani a farko.

Idan wurin ya ishe ki da ƙaiƙayi da ɗashewa ki ɗan daka ki yi mixing da coconut oil ko zaitun ki shafa. Za ki iya shan Man tafarnuwa da shafa shi a ƙasan ki domin kashe kwayoyin cuta, ki rinƙa yin zallan miyan shi da ɗan tarugu kina ci abinci in ba za ki iya amfani da ɗanye ba.

<•> Apple cider Vinegar, wato ruwan khal yana kashe infection da tightening gaban mace, a dafa ruwa a surka a zuba kamar cokali biyu babba a zauna a ciki na minti 10, ko a rinƙa kama ruwa sau biyu ko uku a rana, sannan a rinƙa shan sa a ruwan zafi ko lipton.

<•> Ganyen raihan wato basil yana alamar da zuba ruwa da ma kashe infection, idan babu ɗanyen sai garin a kwaɓa da zuma ko madara ana shan babban cokali sau biyu a rana infection zai tafi.

<•> Ganyen gwaiba maganin infection ne, ki dafa shi ki na sha sau uku a rana zai ji da zuban ruwa ya kuma kashe infection.

<•> Ganyen rumman yana fim da ciwon da sanyan ruwa mai wari da alamar, in an samu fruit din a sha, in ba a samu ba a nemi ganyen a sha da ruwa ko madara kullum da safe kafin breakfast.

<•> Cin ayaba biyu kullum da safe zai taimaka wajen shakatawa da ruwan infection, za ki iya niƙa shi tare da zuma cokali biyu ki sha zai yi har da maganin mata.

<•> Neem, wato dalbejiya ko (Dogon Yaro)maganin kashe kwayoyin cuta ne na ha yaron, ki yi garin sa ki sha tea spoon safe da yamma a cikin madara, ko kuma ki daka danyen sa ki dafa da ruwa na minti goma in ya huce ki rinƙa kama ruwa da shi safe da yamma har sai kin daina jin ƙaiƙayi kuma zuban ruwan ya tsaya.

Haka nan in akwai Ƙuraje sosai ki jajjaga ki zuba coconut oil ko zaitun in babu ki ɗebi zallan sa ki shafa a wuraren da kuraje suka feso na minti 30 sai ki wanke. Ki siyo oil ɗin ki rinƙa bugun a gabanki in da ki ke jin ciwo da ƙaiƙayi, haka nan za ki iya shan tea spoon na man safe da yamma.

<•> Turmeric, wato kurkum yana kashe infection, ki rinqa cin sa abinci ko ki samu madara ki dan kadan dafa ki zuba tea spoon na shi ki sha rabin kofi safe da yamma zai mutu.

Da fatan za’a taimaka domin turawa sauran yan domin su amfana kamar yadda kaima ko kema kuka amfana.