Yadda Ake Warware Sihiri A Musulunce
Tambaya?
Assalamu alaikum Dan Allah malam a fitar dani cikin duhu game da abin da yake damuna. Mahaifiya ta ce ta je gurin malami ai mata naganin ciwon mara da yake damun ta, tace tana da ciki yakai shekara ɗaya, amma likitoci sun yi Scanning sunce ba komai to sai malamin yace mata asiri aka yi mata, kuma zai yi mata magani nan take ta haife abinda yake cikin ta amma za ta kawo tunkiya da dubu bakwai.
To sai mahaifiyar tawa take faɗa min in kawo kudi a sayi tunkiyar kuma akai masa dubu bakwai, to gaskiya malam zuciya ta ba ta aminta da malamin, ba ne shi yasa nike keso ka bani fatawa shin irin wannan hanyar ta magani ta halatta a addini?
Sannan kuma, idan bata halatta ba wacce hanya zan bi wajen ƙin biyan kudin da kuma sanar da ita, saboda ina da matsala, ta bangaren aqeeda mun banbanta. Wassalam nagode malam Allah ya ƙara basira.
Amsa;
To ƴar uwa tabbas ba’a warware sihiri ta hanyar sihiri, sai:dai ana iya warware sihiri ta hanyar ayoyin Alqur’ani, wasu malaman sun yi bayani cewa: ana iya warware sihiri ta hanyar karanta Ayatul-kursiyyu da Kuliya da Iklas da Falaki da Nasi, da kuma aya ta: 117 zuwa ta 122, na suratul A’araf, sai kuma aya ta: 79-81 a suratu Yunus, sannan sai a hada da aya ta: 65-70 a suratu Dhaha, za’a karanta su, sai a tofa a ruwan da aka zuba magarya guda bakwai, sannan ayi wanka da shi.
Amma bai halatta ki taimaka mata ba, wajan bada wadannan kayan da boka ya nema ba, saboda ba’a yiwa iyaye biyayya a wajen sabon Allah.
Ya wajaba ki yi mata nasiha cikin hikima, ki sanar da ita cewa: Annabi Tsira da Amincin Allah su Tabbata a gare Shi yana cewa:” “Duk wanda ya je wajan boka, ya tambaye shi wani abu, Allah ba zai amshi sallar shi ba, ta kawana arba’in” kamar yadda muslim ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 2230.
Bisa ga wadancan bayanai kin ga in mutum ya mutu a wadannan kwanaki akwai matsala, musamman ma tun da akwai hanyar da shari’a ta yarda da ita, a wani hadisin kuma yana cewa: “Duk wanda ya je wajan boka ya gasgata abin da ya fada, to tabbas ya kafurce da abin da annabi Muhammad ya zo da shi” kamar yadda ya zo a Sunanu-abi-dawud hadisi mai lamba ta : 3904, kuma Albani ya inganta shi .
Allah ne mafi sani .
Dr Jamilu Yusuf Zarewa
12/4/2014