Addini

Addu’o’in Neman Arziki Da Taimakon Allah

Domin neman arziki a wurin Ubangiji, sai a yi da wannan addu’a da sauran addu’o’in musulunci ya shar’anta;

“Allahumma ya Farijal hammi, wa ya kashifal gammi, farrij hammiy, wa yassir amriy, warham da’afiy, waqillata hilatiy, warzuqni min haithu la ahtasib.”

Ga kuma wasu;

اللَّهُمَّ إَنِّي أَسْأَلُكَ مِنْ فَضْلِكَ

Allahumma inni as’aluka min fadlika

Ya Allah ina neman falalar ka. [Abu Dawud]

اَللَّهُمَّ اِغْفِرْ لِي وَارْحَمْنِي وَاهْدِنِي وَعَافِنِي وَارْزُقْنِي

Allahumma-ighfir li, warhamni, wa-hdini, wa ‘afini, warzuqni

Ya Allah! Ka gafarta mini, ka yi mani rahama, ka shiryar da ni, ka kiyaye ni daga cutarwa, ka azurta ni da arziki da tsira. [Muslim]