Addini

Yadda Manzon Allah S.A.W Yake Yin Kyauta [Bukhari]

Ibn Abbas ya ruwaito cewa:

Manzon Allah (s.a.w) ya kasance mafi kyauta a cikin mutane, kuma ya kasance yana kai kololuwar kyauta a cikin watan Ramadan idan Jibrilu ya hadu da shi. Jibrilu ya kasance yana haduwa da shi kowane dare na Ramadan domin ya koya masa Alkur’ani. Manzon Allah (ﷺ) ya kasance mafi kyauta, har ma ya fi iska mai qarfi (a cikin shiri da gaggawar yin sadaka).

حَدَّثَنَا عَبْدَانُ، قَالَ أَخْبَرَنَا عَبْدُ اللَّهِ، قَالَ أَخْبَرَنَا يُونُسُ، عَنِ الزُّهْرِيِّ، ح وَحَدَّثَنَا بِشْرُ بْنُ مُحَمَّدٍ، قَالَ أَخْبَرَنَا عَبْدُ اللَّهِ، قَالَ أَخْبَرَنَا يُونُسُ، وَمَعْمَرٌ، عَنِ الزُّهْرِيِّ، نَحْوَهُ قَالَ أَخْبَرَنِي عُبَيْدُ اللَّهِ بْنُ عَبْدِ اللَّهِ، عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ، قَالَ كَانَ رَسُولُ اللَّهِ صلى الله عليه وسلم أَجْوَدَ النَّاسِ، وَكَانَ أَجْوَدُ مَا يَكُونُ فِي رَمَضَانَ حِينَ يَلْقَاهُ جِبْرِيلُ، وَكَانَ يَلْقَاهُ فِي كُلِّ لَيْلَةٍ مِنْ رَمَضَانَ فَيُدَارِسُهُ الْقُرْآنَ، فَلَرَسُولُ اللَّهِ صلى الله عليه وسلم أَجْوَدُ بِالْخَيْرِ مِنَ الرِّيحِ الْمُرْسَلَةِ‏.‏

Dubawa: Sahihul Bukhari 6
Acikin littafin: Littafi na 1, Hadisi na 6