Addini

Yadda Ake Yin Sallar Jana’iza A Musulunci

Yadda ake yin sallar jana’iza wa mamaci a cikin addinin Musulunci.

  1. KABBARA TA FARKO; Ana karanta (suratul fatiha) ne kawai banda wata sura ko wata aya.
  2. KABBARA TA BIYU; Ana karanta salatin Annabi ne kawai ba wani salati na daban ba.
  3. KABBARA TA UKU; Anayin addu’a ga wanda Ya mutu mace ko namiji.
  4. KABBARA TA HUDU; Zaka yi addu’a ne ga sauran Al’ummar musulmi waɗanda suke raye da matattu.

Ɗan uwa kana Gamawa sai ka jira liman yayi sallama. Ita kuma sallamar guda ɗaya ce tak! Kuma zaka yi tane a bangaren hannun damar ka.

Allah muke roko da ya kara tabbatar damu akan sunnar Manzon Allah (S.A.W).