Addini
Tarihin Annabi Idris A.S
An haifi Annabi Idris A.S kuma ya girma a Babila bisa koyarwa da addinin Annabi Adamu da ɗansa Shitu. Annabi Idris shine ƙarni na biyar na Annabi Adamu. Ya kira jama’a su koma addinin kakanninsa, amma ‘yan kadan ne suka saurare shi, yayin da mafi rinjaye suka bijire.
Annabi Idris da mabiyansa sun bar Babila zuwa Masar. A nan ne ya ci gaba da aikin sa, yana kiran mutane zuwa ga adalci da gaskiya, yana karantar da su wasu salloli da kuma umurce su da yin azumin wasu ranaku da bayar da wani kaso na dukiyar su ga fakirai.
Nassosin Alkur’ani:
Abubuwan da suka shafi Alqur’ani na wannan labarin.
Suratut 19: aya ta 56
Suratut 21:85