Wane Ne Musuluncin Shi Ya Fi Kyau A Cikin Musulmai? [Bukhari]

Abu Musa ya ruwaito:

Wasu mutane sun tambayi Manzon Allah (SAW) cewa: “Musuluncin waye ya fi kyau? watau (wane ne musulmin kwarai)?” Sai ya karba masa da cewa: “Wanda ya nisanci cutar da musulmi da harshen shi da hannun shi”.

حَدَّثَنَا سَعِيدُ بْنُ يَحْيَى بْنِ سَعِيدٍ الْقُرَشِيِّ، قَالَ حَدَّثَنَا أَبِي قَالَ، حَدَّثَنَا أَبُو بُرْدَةَ بْنُ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ أَبِي بُرْدَةَ، عَنْ أَبِي بُرْدَةَ، عَنْ أَبِي مُوسَى ـ رضى الله عنه ـ قَالَ قَالُوا يَا رَسُولَ اللَّهِ أَىُّ الإِسْلاَمِ أَفْضَلُ قَالَ ‏ “‏ مَنْ سَلِمَ الْمُسْلِمُونَ مِنْ لِسَانِهِ وَيَدِهِ ‏”‏.

Duba: Sahihul Bukhari 11
Acikin littafin: Littafi na 2, Hadisi na 4