Yadda Saɓani Kan Shugabanci Ya Kai Ga Kafuwar Shi’a Da Sunnah
Magajin Annabi Muhammadu (Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) shine babban batu da ya raba al’ummar musulmi zuwa kashi da dama a karni na farko na tarihin Musulunci bayan rasuwar Annabi, inda mafi shahara a cikin wadannan mazhabobi su ne rassan Musulunci na Shi’a da Sunnah.
Bayan rasuwar Annabi Muhammadu (S.A.W) a shekara ta 632, wasu gungun Musulmai sun yi imani cewa Abu-Bakr, abokin Annabi (S.A.W) na kusa ya kamata ya zama Halifa na farko. Wannan ita ce mahangar Ahlus-Sunnah. Wasu tsiraru sun yi imanin cewa Sayyiduna Aliyu, surukin Annabi (S.A.W) ne ya kamata ya jagoranci al’umma.
An san wadannan musulmi na bangaren Aliyu da sunan Shi’a, wanda ke nufin ‘Jam’iyyar Aliyu’. A karshe aka nada Abubakar Halifa na farko. Tun da farko Aliyu bai yi mubaya’a ga Abubakar ba. Bayan ‘yan watanni, kuma bisa ga akidar Sunnah da Shi’a, Aliyu ya canza ra’ayin shi ya yarda da Abubakar, domin ya kiyaye dunkulewar sabuwar daular Musulunci.
Rarrabawa tsakanin ‘yan Sunnah da Shi’a ita ce mafi girma kuma mafi dadewa a tarihin Musulunci. Membobin ƙungiyoyin biyu sun kasance tare har tsawon ƙarni kuma suna yin imani da ayyuka masu yawa. Amma sun bambanta a koyarwa, al’ada, shari’a, tiyoloji da tsarin addini.
Kalmar ‘Sunni’ tana da alaqa da kalmar larabci Sunnah kuma tana nufin ‘mabiya Sunnar Annabi ko hadisai’. Ahlus-Sunnah su ne mafi rinjayen musulmin duniya. Kalmar ‘Shi’ah’ ta fito ne daga jumlar da ke nufin ‘mabiya Aliyu’. Aliyu shi ne surukin Annabi (S.A.W).