Addini

Mutumin Da Ya Je Kai Ƙorafin Sifikar Masallaci Na Damun Shi Ya Musulunta

Bikin Sallar Idi a ranar Asabar, Hussin Goss, shugaban masallacin Cold Coast, a kasar Austaraliya ya samu ziyarar wani dattijo yana korafin hayaniya daga masallaci.

Mutumin da ya fito daga wani gidan jinya da ke kusa, Goss yayi masa maraba, yayi amfani da damar ya ba shi abinci yayi masa magana game da addinin Musulunci.

Bayan ‘yan mintoci kadan, mutumin ya yanke shawarar karbar addinin Musulunci, yana karanta shahada a tsakanin musulmin da suka zo bikin ‘Eid Al-Fitr’.

Goss sananne ne a cikin al’ummar musulmin yankin Gold Coast, wanda ya kasance shugaban kungiyar Islama na tsawon shekaru 29.

A ’yan shekarun da suka gabata, gidauniyar agaji ta musulmi ta ba shi takardar shaidar yabo saboda taimaka wa “samar da sauyi a rayuwar marasa galihu”.

A halin yanzu akwai musulmi kusan 10,000 da ke zaune a fadin yankin, inda kusan 1200 daga cikinsu ke halartar salla a masallacin.

Goss ya yaɗa wani bidiyo a Instagram da ke nuna wani mutum yana karbar Musulunci a daren Lailatul kadari, a ranar 27 ga Ramadan.