Addini

Mutum Ne Yayi Buɗa Kaki Da Jima’i A Ramadan, Mene Ne Hukunci?

Tambaya?

Assalamu alaykum, Mallam barka da warhaka dafatan kana lafiya.

Malam mene ne hukuncin wanda yayi azumi amma bai yi buɗa baki ba, ma’ana bai sha ruwa bayan ladan ya kira sallar Magriba ba. Sai yayi jima’i da matar shi. Ya azumin shi yake?.

Amsa;

Wa’alaikumus-salam. Azumin shi yayi daidai, mutukar ya sadu da matar shi ne bayan rana ta faɗi.

Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallama yayi umarni ayi buɗa baki da Dabino ga wanda ya samu dama, in ba hali kuma ayi da ruwa kamar yadda ya tabbata a hadisai.

Abin da ya gabata yana nuna cewa; Yin buɗa baki da Dabino ko ruwa shi ne sunna, sai dai wanda ya fara da jima’i azumin shi ya inganta, tun da Allah ya halatta masa jima’i a daidai wannan lokacin kamar yadda aya ta: 187 a suratul Bakara ta nuna hakan.

Allah ne mafi sani.

Dr Jamilu Zarewa
1/07/2016