Labarin Annabi Salih A.S
Sai Allah Ya aiko musu da Annabinsa Salihu, mutum daga cikinsu. Sunansa Salih Ibn Ubeid, Ibn Maseh, Ibn Ubeid, Ibn Hader, Ibn Samud, Ibn Ather, Ibn Eram, Ibn Nuhu.
Annabi Salihu A.S ya kira mutanensa zuwa ga bauta wa Allah Shi kadai, kuma kada su yi shirka da Shi. Duk yake wasu daga cikinsu sun yi imani da shi, amma akasarinsu suka kafirta kuma suka cutar da shi ta hanyar magana da aiki.
Annabi Salihi A.S ya umurce su da cewa: “Ya ku mutanena! Ku bauta wa Allah, ba ku da wani abin bautawa face Shi.” Ayah 11:61
Annabi Salih A.S ya shahara da hikima da tsarkinsa da kyautatawa kuma mutanensa sun kasance suna girmama shi sosai kafin wahayin Allah ya zo masa. Mutanen Salih A.S suka ce masa: “Ya Salihu! Ka kasance a cikin mu a kan kyakkyawan fata (kuma mun yi nufin ka zama shugaban mu), har zuwa wannan sabon abu da ka zo da shi, cewa mu bar gumakanmu, kuma mu bautawa Allah Shi kaɗai! Shin, kai (yanzu) Ka hana mu bauta wa abin da ubanninmu suka kasance sunã bautãwa? Qur’an 11:62