Addini

Kwanan Watan Haihuwar Annabi S.A.W

Yana daga cikin hikimar Allah Madaukakin Sarki boye kwanan watan haifuwar ManzonSa ga al’ummar Musulmi.

Nassi ya tabbata cikin Sahihu Muslim daga Manzon Allah mai tsira da amincin Allah cewa ya ce an haife shi ne a ranar litinin. Amma babu wani nassi da ya inganta daga gare shi cewa ga watan da aka haife shi, ko ga kwanan watan da aka haife shi; wannan shi ne ya sa malam tarihi suka yi sabani da yawa game da cikin watan da aka haife shi da kuma kwanan watan da aka haife shi bisa zantuttuka da yawa.

Wasu suka ce: An haife shi ne a ranar biyu ga watan Rabi’ul Awwal.

Wasu suka ce: An haife shi ne a ranar uku ga watan Rabi’ul Awwal.

Wasu suka ce: An haife shi ne a ranar takwas ga watan Rabi’ul Awwal.

Wasu suka ce: An haife shi ne a ranar tara ga watan Rabi’ul Awwal.

Wasu suka ce: An haife shi ne a ranar goma ga watan Rabi’ul Awwal.

Wasu suka ce: An haife shi ne a ranar goma sha biyu ga watan Rabi’ul Awwal.

Wasu suka ce: An haife shi ne a ranar goma sha bakwai ne ga watan Rabi’ul Awwal.

Wasu suka ce: An haife shi ne a ranar ishirin da biyu ga watan Rabi’ul Awwal.

Wasu suka ce: An haife shi ne cikin watan Ramadan.

Wasu suka ce: An haife shi ne cikin watan Safar.

Wasu suka ce: An haife shi ne cikin watan Rabi’ul A’akhir.

Ya Allah muna rokon Ka Ka yi wa Annabi salati da tsira tare da iyalansa da shabbansa da dukkan wadanda suka bi su da kyautayi. Ameen.

Dr. Ibrahim Jalo Jalingo