Izala Ta Gargaɗi Dr. Jalo Jalingo Kan Hadisan Iyayen Annabi S.A.W

Kungiyar Jama’atu Izalatul Bid’ah Wa Iqamatul Sunnah ta kasa a Najeriya ta yi gargaɗi tare da dakatar da ɗaya daga cikin membobin ta, Dr. Ibrahim Jalo Jalingo daga wani cigaba da wani karatu da yake yi wanda yake jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin al’ummar game da iyayen Annabi Muhammad (Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi).

Idan zai zamu iya tunawaƴan kwanakin nan dai an sha ganin bidiyo na malamin a shafukan sada zumunta inda yake bayani kan makomar iyayen Annabi, wanda wannan batu ya ja zazzafar muhawara tsakanin ɗaliban ilimi da malamai da mabiya.

A yayin wani taro da ƙungiyar ta yi a sakateriyar ƙungiyar da ke Abuja babban birnin Najeriya ranar Alhamis, ƙungiyar ta ce ta dakatar da tattauna wannan matsala ko rubutu dangane da ita a shafin intanet domin wannan matsala, lamari ne da ya shafi malamai da ɗaliban ilimi.