Hukuncin Masu Satar Mutane A Cikin Musulunci

Assalamu alaikum warahamatullahi, a yau zamu kawo muku fatawa akan hukuncin masu satar mutane domin kuɗin fansa a cikin addinin Musulunci tare da Sheikh Ibrahim Jalo Jalingo.

Mallam ya ce;

  1. Hukuncin masu satar da mutane a cikin Musulunci shi ne: A karkashe su, ko a giggicciye su, ko a yayyanke hannayen su da kafafuwan su a bisa sabani har azaba da raɗaɗi ya kashe su, ko kuwa a haramta musu zama cikin kasar su.

  2. ﴿ إِنَّمَا جَزَاءُ الَّذِينَ يُحَارِبُونَ اللَّهَ وَرَسُولَهُ وَيَسْعَوْنَ فِي الْأَرْضِ فَسَادًا أَن يُقَتَّلُوا أَوْ يُصَلَّبُوا أَوْ تُقَطَّعَ أَيْدِيهِمْ وَأَرْجُلُهُم مِّنْ خِلَافٍ أَوْ يُنفَوْا مِنَ الْأَرْضِ ۚ ذَٰلِكَ لَهُمْ خِزْيٌ فِي الدُّنْيَا ۖ وَلَهُمْ فِي الْآخِرَةِ عَذَابٌ عَظِيمٌ﴾. سورة المائدة: ٣٣.
  3. Muna kara jan hankalin dukkan jami’an tsaron mu da su kafurce wa ragwanci akan masu garkuwa da mutane, su zabura su kara nuna kishin kasar su da al’ummar su, su bi wadannan miyagu a duk inda suke cikin garurura da dazukan Najeriya su karkashe su, ko su kakkama su; domin kasa ta samu zama lafiya.

Daga: Dr. Ibrahim Jalo Jalingo