Addini

Banbancin Mushrikan Yanzu Da Na Farko

Mushrikan farko sun yarda da Rububiyya kuma Qur’ani ya tabbatar da haka.

Allah ya ce:
وَلَئِن سَأَلْتَهُم مَّنْ خَلَقَ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ لَيَقُولُنَّ اللَّهُ ۚ

“Da za ka tambaye su waye ya halicci sammai da ƙasa, tabbas za su ce Allah (ne ya Halicce su)”.

Sai dai a Uluhiyya ne suka samu matsala, shi yasa suke ganin ta yaya za’a ce a aje gumaka da yawa a bauta ma Ubangiji ɗaya, su a wurin su yin hakan abin mamaki ne aka zo da shi.

أَجَعَلَ الْآلِهَةَ إِلَٰهًا وَاحِدًا ۖ إِنَّ هَٰذَا لَشَيْءٌ عُجَابٌ

“Shin, ya sanya gumaka duka abin bautawa guda?Lallai wannan hakika abu ne mai ban mamaki”.

Su kuma mushrikan yanzu har Rububiyyar sun dauka sun ba halittu, inda zaka ga an dauki aikin da na Allah ne amma sai a mika ma wani bawa shi.

Allah ya ganar da mu gaskiya ya kuma bamu ikon bin ta cikin kowane yanayi.