Addini

Babban Malamin Iran Ayatollah Reyshahri Ya Rasu

An kwantar da shi a asibitin Khatam-al-Anbya na Tehran kuma ya rasu da sanyin safiyar Talata yana da shekaru 75.

An haife shi ga dangin addini a Shahr-e-Rey a shekara ta 1946. Bayan kammala karatun firamare, ya halarci makarantar hauza a unguwar su kafin ya tafi makarantar hauza ta Kum bayan yan shekaru. Ya zama daya daga cikin manyan malamai a cibiyar.

Reyshahri shi ma dan juyin juya hali ne kuma tsarin leken asirin gwamnatin Pahlavi ya kama shi sau da yawa saboda yakar shi da gwamnatin.

Bayan juyin juya halin Musulunci a shekarar 1979 ya dauki mukamai da dama a bangaren shari’a a matsayin shugaban kotuna daban-daban. Ya kasance ministan leken asiri na farko na Jamhuriyar Musulunci a shekarar 1984.

Ayatullah Reyshahri kuma ya kasance memba a majalisar kwararru a lokuta da dama.