Babban Haɗarin Da Ke Cikin Yawan Yin Zato

Ɗaya daga cikin magabatan mu, na wannan al’umma ta Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya bayyana irin haɗarin da ke tattare da yawan zato.

Abdullahi bn Mas’ud – Allah Ya yarda da shi – ya ce:

Wanda aka yi masa sata zai ci gaba da yin zargi da zato (game da wanda yayi masa satar) har ya sai zama cewa shine mafi muni fiye da barawon da yayi masa satar.

Al-Bukhari, Al-Adab Al-Mufrad Lamba: 1289. Albani ya inganta isnadinsa sahih a cikin Sahih Al-Adab Al-Mufrad na: 974.

Allah shine mafi sani!