Addini

Ban Son Shan Azumin Ramadan, Ko Zan Iya Shan Maganin Hana Haila?

Tambaya?

Assalamu alaikum,
Allah ya gafarta malam, azumin watan Ramadan, ya zo ni kuma ba na son in sha ko azumi ɗaya, to shi ne na sayi maganin da zai hanani yin al’ada na sha, bayan mun hadu da kawata, sai take ce min wai babu kyau, shi ne na ce mata ban yarda ba, zan tambayi malamai, don Allah malam a kara min bayani?

Amsa;

Wa’alaykumussalam,
To ƴar uwa amfani da maganin da yake hana haila, wato magungunan saka tazarar haihuwa (Contraceptive Pills or Injection) ya halatta, Idan ya zama ba zai cutar ba, amma idan zai cutar, to ya haramta saboda fadin Allah “kar ku jefa kawunan ku a cikin halaka” suratu Albakarah aya ta 195.

Sai dai duk da cewa hakan ya halatta da sharudan da suka gabata, amma barin maganin shi ya fi kyau, sai idan bukatar hakan ta taso, saboda mutum ya zauna akan yadda yake ya fi masa kwanciyar hankali akan yayi abin da zai canza dabi’ar shi, musamman ma wasu daga cikin kwayoyin (Birth Space Pills) na zamani suna dagula kwanakin haila (Menstruation Period), kamar yadda ya bayyana gare mu, sai a kiyaye.

Don neman karin bayani, duba: Dima’uddabi’iyya shafi na : 54 .

Allah ne mafi sani.

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA

22\6\2015