Addini

An Dawo Itikafi Masallatai Masu Tsarki Biyu Bayan Shekaru 2 Q Saudiyya

Za a cigaba da gudanar da Itikafi ne a cikin watan Ramadan mai zuwa bayan shafe shekaru biyu.

Dr. Abdul Rahman Al-Sudais, shugaban fadar shugaban kasa mai kula da harkokin masallatai biyu ne ya sanar da hakan.

Al-Sudais yace nan ba da dadewa ba fadar shugaban kasa za ta fara bayar da izini ta shafin ta na intanet, kuma hakan zai yi daidai da takamaiman sharudda da ta gindaya.

Itikaf, al’adar zama a cikin masallaci kawai don ibada da tunani, an dakatar da ita a masallatan Harami guda biyu a cikin watan Ramadan na 2020 sakamakon barkewar cutar ta Covid-19. An cigaba da dakatar da yin Itikafi a cikin watan Ramadan na shekarar 2021 a matsayin matakin riga-kafi don dakile yaduwar cutar Coronavirus.

Kimanin masallata 100,000 ne suka saba yin itikafi a masallatan biyu a cikin kwanaki 10 na karshen watan Ramadan.