Alkur’anin Da Sayyidina Usman Ke Karantawa Lokacin Da Aka Kashe Shi

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah madaukakin sarki, mai girma da buwaya.

A yau zamu nuna wa masu karatu wasu abubuwa na tarihi a lokacin sahabin Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), wato Sayyidina Usman (Allah Ya Kara Masa Yarda).

Kamar yadda kowa ya sani a tarihi, Sayyidina Usman a lokacin da yake Khalifanci wasu ya ta’adda sun tsallako a gidan shi a lokacin sun same yana karatun Alqur’ani mai girma, inda suka kai masa hari yana tsakiyar karanta wata aya acikin suratul Bakra mai cewa;

Fassara

"Da sannu Allah zai yi maka sakayya, Shi mai ji ne, kuma Masani".

Yana karanta wannan ayar ne suka kai masa hari har yan ta’addan suka sare hannun matar shi, kafin su hare shi. Kamar yadda kuke a kan Alkur’anin akwai wani abu ja, wanda aka bayyana cewa shine jinin Sayyiduna Usman ne da fallatsa akan Alkur’anin.

Wannan Alkur’anin yana ajiye a wuraren tarihi a ƙasar Saudiyya a yanzu.