Abin Sani Game Da Ƴan Uwan Annabi Yusuf A.S
Abin sani game da labarin ‘yan uwan Annabi Yusuf (A.S), malaman Musulunci suna da fahimta uku akan matsayin wadannan bayin Allah:
- Cewa Annabawa ne
- Ba Annabawa ba ne
- Duk fahimtar da aka dauka tayi
Cewa Annabawa Ne
Manyan malaman Musulunci sun yi rubutu mai yawa akan abin da ya shafi labarin ‘yan uwan Annabi Yusuf maza, cewa lalle dukkan su “Annabawan Allah ne”. Wani daga cikin malaman shi ne Ibn Zaid, da Imamul Bagawi da sauran malamai.
Cewa Ba Annabawa Ba Ne
Da yawan makaman sun tafi akan wannan fahimtar, kamar ibn Taimiyyah, Imamul Qurdabi, Fakhrud-deen Al-Razi, Ibn Katheer (Allah ya gafarta musu) da sauran malamai.
Duk Fahimtar Da Aka Ɗauka Tayi
Da yawan wasu daga cikin malaman tarihi da na Tafsiri sun tsaya tsakiya a iya fahimtar su kowa yana da tashi madogara, kuma duk wacce aka dauka tayi daidai, kamar Abi-Laith Al-Wahidy, ibn-Jauzy da Alqady Iyadh (Allah ya gafarta musu) da sauran wasu malamai.
Allah ne mafi sani.
Rubutawar Mallam Muhammad Mujahid