Abin Da Ya Kamata Ka Sani Kafin Ka Saki Matar Ka Saki 3

Nafi’i ya ruwaito cewa: “Wani mutum ya zo wajen Ibn Umar Allah Ya yarda da shi, sai ya tambayi wani mutum da ya saki matar shi har sau uku, sannan ya aurar da ita ga dan’uwan shi, ba tare da wata yarjejeniya ba daga gare shi, domin ya yi. ta halalta masa kuma. Shin ta halatta ga mijin farko? Ibn Umar ya ce, “A’a, sai dai idan aure ne ta so. Mun kasance muna daukar wannan haramtaccen fasiqanci a zamanin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama”.

Source: al-Sunan al-Kubrá lil-bayhaqi 14189

Daraja: Sahih ( ingantacce) a cewar Al-Dhahabi

ﻋَﻦْ ﻧَﺎﻓِﻊٍ ﺃَﻧَّﻪُ ﻗَﺎﻝَ ﺟَﺎﺀَ ﺭَﺟُﻞٌ ﺇِﻟَﻰ ﺍﺑْﻦِ ﻋُﻤَﺮَ ﺭَﺿِﻲَ ﺍﻟﻠﻪُ ﻋَﻨْﻪُ ﻓَﺴَﺄَﻟَﻪُ ﻋَﻦْ ﺭَﺟُﻞٍ ﻃَﻠَّﻖَ ﺍﻣْﺮَﺃَﺗَﻪُ ﺛَﻠَﺎﺛًﺎ ﻓَﺘَﺰَﻭَّﺟَﻬَﺎ ﺃَﺥٌ ﻟَﻪُ ﻋَﻦْ ﻏَﻴْﺮِ ﻣُﺆَﺍﻣَﺮَﺓٍ ﻣِﻨْﻪُ ﻟِﻴُﺤِﻠَّﻬَﺎ ﻟِﺄَﺧِﻴﻪِ ﻟَﻪُ ﺗَﺤِﻞُّ ﻟِﻠْﺄَﻭَّﻝِ ﻗَﺎﻝَ ﻟَﺎ ﺇِﻟَّﺎ ﻧِﻜَﺎﺡَ ﺭَﻏْﺒَﺔٍ ﻛُﻨَّﺎ ﻧَﻌُﺪُّ ﻫَﺬَﺍ ﺳِﻔَﺎﺣًﺎ ﻋَﻠَﻰ ﻋَﻬْﺪِ ﺭَﺳُﻮﻝِ ﺍﻟﻠﻪِ ﺻَﻠَّﻰ ﺍﻟﻠﻪُ ﻋَﻠَﻴْﻪِ ﻭَﺳَﻠَّﻢَ

14189 ﺍﻟﺴﻨﻦ ﺍﻟﻜﺒﺮﻯ ﻟﻠﺒﻴﻬﻘﻲ ﺑﺎﺏ ﻣﺎ ﺟﺎﺀ ﻓﻲ ﻧﻜﺎﺡ ﺍﻟﻤﺤﻠﻞ

6/2782 ﺍﻟﻤﺤﺪﺙ : ﺍﻟﺬﻫﺒﻲ ﺧﻼﺻﺔ ﺣﻜﻢ ﺍﻟﻤﺤﺪﺙ :