Lafiya

Maganin Karfin Azzakari: Abin Da Ya Kamata A Lura Da Shi

Namijin da yake fama da raunin al’aura ba’a cewa ya sha magani kaza, sai anyi masa bincike guda uku. Abu na farko shine za’a duba a gani baya da ciwon suga? Saboda cutar sugar tana sabbabar da raunin al’aura. Idan yana da ciwon sugar a kwai maganin da zaiyi amfani da shi.

Abu na biyu shine za’a duba yana da basir? Idan yana da shi akwai hanyoyin da ake bi a magance shi.

Abu na uku shine za’a duba a gani baya da gajiya da talauci? Ko yawan aiki ko damuwa domin shima yana kawo raunin al’aura saboda hankalin bai natsuba balle yayi sha’awar jima’i mai kyau ba.

Abubuwan da za’a haɗa

Ciwon suga

○ Man Hulba
○ Zaitu (Jonifer Oil)
○ Habba Yar’ Algeriya
○ Zaitu Lauz

Za’a hada su waje daya kafi ya kwanta da dare da awa daya zai samu madara musamman na luna, sai a dumama su tare da zuma sai a gauraya shi a sha. Da safe kuma kafin a karya.

Maras ciwon suga

Ga waɗanda kuma basu da ciwon suga yana son ya samu kusancin matar shi sai ya samo Hulba tare da matan zasu sha tare kafin su kwanta da awa daya wanna yana taimakawa.

Daga karshe ya kamata a rage duk abubuwan da suke kawo damuwa sosai da kuma shan suga fiye da ƙima.