Jerin Sunayen Tsofaffin Gwamnonin Jihar Kano (1967-2023)
Wannan shine jerin sunayen waɗanda suka gudanar da mulkin soja da gwamnoni jihar Kano.
An kafa jihar Kano ne a ranar 27 ga Mayun 1967 lokacin da aka raba yankin Arewa zuwa jihohin Benue-Plateau, Kano, Kwara, Arewa-Tsakiya, Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma.
Kwamishinan ’Yan sanda, Audu Bako: Yayi gwamnan (Mayu 1967 Yuli 1975) mulkin Soja.
Kanar Sani Bello: Yayi gwamnan Soja (Yuli 1975 Sept 1978).
Captain Ishaya Shekari: Yayi gwamnan Soja (Sept 1978 Oct 1979.
Alhaji Muhammadu Abubakar Rimi: Yayi gwamna (Oktoba 1979 May 1983) karkashin jam’iyyar PRP.
Alhaji Abdu Dawakin Tofa: Yayi gwamna (Mayu 1983 zuwa Oktoba 1983) a PRP.
Alhaji Sabo Bakin Zuwo: Yayi gwamna (Oktoba 1983 zuwa Disemba 1983) a PRP.
Air Commodore Hamza Abdullahi: Yayi Gwamna (Janairu 1984 zuwa Agusta 1985) mulkin Soja.
Kanal. Ahmed Muhammad Daku: Yayi gwamnan Soja (Agusta 1985 zuwa 1987).
Captain Mohammed Ndatsu Umaru: Yayi gwamnan Soja (Disamba 1987 zuwa 27 Yuli 1988).
Kanar Idris Garba: Yayi gwamnan Soja (Agusta 1988 zuwa Janairu 1992).
Architect Kabiru Ibrahim Gaya: Yayi gwamnan (Janairu 1992 zuwa Nubamba 1993) a jam’iyyar NRC.
Kanar Muhammadu Abdullahi Wase: Yayi gwamnan soja (Disemba 1993 zuwa Yuni 1996).
Kanar Dominic Oneya: Yayi gwamnan soja (Agusta1996 zuwa Satumba 1998).
Kanar Aminu Isa Kontagora: Yayi gwamnan Soja (Satumba 1998 zuwa Mayu 1999).
Injiniya (Dr.) Rabiu Musa Kwankwaso: Yayi Gwamna (Mayu 1999 zuwa Mayu 2003) a PDP.
Malam Ibrahim Shekarau: Yayi Gwamna (Mayu 2003 zuwa Mayu 201) a ANPP.
Injiniya (Dr.) Rabiu Musa Kwankwaso: Ya sake yin gwamna (Mayu 2011 zuwa Mayu 2015) a PDP.
Abdullahi Umar Ganduje: Yayi gwamna (Mayu 2015 zuwa Mayu 2023).