Takaitaccen Tarihin Dr. Abdallah Usman Umar Gadon Kaya
Malam haifaffen garin Gombe ne (Kumo), Mahaifinsa kuma dan Giade ne (Bauchi) Shi ne farkon wanda ya kai Izala garin Giade.
Daga baya karatu ya zaunar da Malam a Kano.
Malam yayi karatu a Makarantar Legal ta Kano kafin tafiyar shi Madina.
Hakanan, Malam yayi karatu a wurin Malamai da dama, ya kuma bi zaurukan Malamai ya dauki ilimi. Daga cikin Malaman shi akwai;
– Sheikh Dr. Ahmad Ibrahim Bamba (Rahimahulla).
– Sheikh Abdulwahab Abdallah.
– Sheikh Ja’afar Mahmud Adam (Rahimahullah)
– Sheikh Dr. Muhammad Sani R/Lemo.
– Sheikh Dr. Bashir Aliyu Umar.
– Sheikh Dr. Muhammad Sani B/Kudu da sauran su.
Malam mahaddacin Alkur’ani ne, wanda Allah ya ba wa daddadan sautin karatun shi.
Malam yaje Madina yayi karatu a Kulliyatul Hadis, kamar yadda ya bibiyi wasu daga cikin majalisan Malaman wannan gari ya kwankwadi ilimi daga gare su.
Bayan dawowar Malam daga Madina, ya dora Masters a Jami’ar Bayero ta Kano.
Malam yaje kasar Sudan inda ya yi PhD ɗin shi a can.
Malam mutum ne me son ilimi da daliban ilimi, da kokarin karantar da shi. Kamar yadda Allah ya hore masa lafiyar fita yada da’awa a sassan wannan kasa da ma makotan kasashe.
Malam mutum ne, me kyawawan dabi’u, wanda duk wanda ya zauna da shi zai fahimci haka. Ta yadda yake jan dalibansa a jiki sosai, da shiga cikin lamuran su.
Malam Limami ne a Masallacin Usman Bn Affan Gadan Kaya.
Kasancewar Malam karantarwa ya sa a gaba, hakan ta sa ya karantar da litattafai da dama a fannoni daban-daban, daga cikinsu akwai;
1. Umdatul Ahkam
2. Bulugul Maram
3. Riyadus Salihin
4. Sunut Tirmizi
5. Iziyya
6. Risala
7. Addurratul Bahiyya
8. Waraqat
9. Alwadhih fi Usulul Fiqh
10. Alqawa’idul Fiqhiyya
11. Usulus salasa
12. Alkawa’idul Arba’a
13. Kitabut Tauhid
14. Usulus Sunna na Ahmad
15. Kashfusshubhat
16. Aqidutud Dahawiyya
17. Aqidutul Wasidiyya
18. Juz’ul Kira’a Khalfal Imam
19. Alfiyatus Suyudi ta hadisi.
20. Alba’isul Hasis
21. Sharhus sunna na Barbahari
22. Alqawa’idul Musla
23. Kitabul kaba’ir
24. Muktasarus Sira
25. Tahzibus Sira na Nawawi.
26. Arba’una Hadisan
27. Attabsira fi Ulumil Qur’an.
28. Hilyatu Dalibil ilmi
29. Ta’alimul Muta’allim
30. Usulus Sunna na Humaidiy
31. Sharhus sunna na Muzani
31. Aqidatud Raziyayn
32. Sarihus Sunna na Dabari
33. Qasidatul Ha’iyya
34. I’itiqad ahlis sunna na Isma’eeliy
35. Almanzumatur Ra’iyya
36. Al’iqtisad fil i’itiqad
37. Lum’atul I’itiqad
38. Almanzumatul Lamiyya
39. Al’aqidatus saffariniyya.
40. Fadhlul Islam
41. Aljami’u li’ibadatil llahi wahdahu
42. Almasa’ilul Jahiliyya
43. Ma’anad Dagut
44. Ma yatamayyazu bihil Muslim anis shirk
45. Nawaqidul islam.
46. Hisnul Muslim.
47. Sharh Usulil Iman na Usaimin
48. Haqiqatus Shi’a na Mausiliy
49. Alfusul fis sira na Ibn Kasir
50. Usulul iman na Ibn Abdulwahhab.
51. Qasidatud Tauba ta Ilbiriy
52. Unwanul Hikam
53. Maqaddimatu usulit Tafsir
54. Ajurrumiyya
55. I’itiqad ahlis sunna fif sahaba
56. Alqaulul Mubeen fi hukmi takfiril Mu’umin
57. Hukmut taswib fi azanil fajr.
Wadannan wasu ne daga cikin littafan da Malam ya karantar, yanzu kuma yana karanatar da;
– Tafsirul Jalalain
– Raudhatun Nazir na Maqdisi
– Muwadda Malik
– Aljauharatul farida
– Alfiraq wal mazahibul islamiyya
– Almu’allaqatus saba’a
– Muktasar Zadul Ma’ad
– Tadribur Rawiy
– Sahihul Bukhari
– Nailu Audar na Shaukaniy
– Sharh Shuzuruz Zahab
– Buhusun fi usulit Tafsir na Fahad Arrumiy.
Daga: Dalibin Malam. Abu Abdurrahman Aminu Garba Adam