Tsohon Shugaban Majalisar Wakilan Najeriya, Ghali Umar Ya Rasu

Tsohon kakakin majalisar wakilai ta 4, Ghali Umar Na’abba ya rasu.

Arewa Times Hausa ta samu labarin cewa ya rasu ne a safiyar ranar Laraba yana da shekaru 65 bayan ya yi fama da rashin lafiya.

An zabi Na’abba daga jihar Kano a matsayin dan majalisar wakilai a shekarar 1999.

Ya zama shugaban majalisar ne watanni kadan bayan kaddamar da majalisar bayan murabus din kakakin majalisar na wancan lokacin, Salisu Buhari daga jihar Kano, bisa badakalar satifiket na jabu.

Kwanan nan ya fice daga jam’iyyar All Progressives Congress, APC, ya koma babbar jam’iyyar adawa ta People’s Democratic Party PDP.