Maganin Amosanin Kai Na Gargajiya

Masu tambayar maganin amosanin kai,

Ga amsa:

Matukar ka tabbatar da wadannan abubuwa uku a tattare da kai, to kana dauke da cutar amosarin kai.

  1. Fitar farin gari-hari a kan ka idan suma ta taru.
  2. Yawan ƙaikayin kai da zubewar sumar kai.
  3. Ciwon kai da zarar ka tara suma.

Ga yadda za’a yi:

A nemi lemon tsami guda biyu a yanka su, amatse ruwan, sai a samu zuma sahihi sai ja cikin sirijin allura uku, sannan a gauraya su sosai.

Sai aske suma gaba daya , sai a shafe kan gaba daya har fuska, amma a kula karya shiga ido, sai a bar shi tsawon awa daya, sannan a wanke ko ina.

InSha Allah in dai za’a yi haka tsawon kwanaki biyar, idan anyi yau kar a yi gobe, za’a ga waraka.