Maganin Ciwon ‘Shawara Da Olsa’ Na Gargajiya

Kamar yadda muka sani, ciwon shawara ‘Typhoid’ da olsa ‘Gymbon ciki’ (Ulcers) suna ɗaya daga cikin rashin lafiyoyin dake ciwa mutane tuwa a kwarya, Musamman a ƙasashe masu tasowa na nahiyar Afirka.

Olsa da Tayifot ko shawara, cututtuka ne masu wuyar sha’ani idan aka bar su suka jima ba’a yi maganinsu ba.

Haka zalika, cututtuka ne dake iya barazana ga rayuwar mutanen dauke da su a wasu lokutan.

Don haka, a yau zamu bayyana muku wadansu hanyoyi na gargajiya masu mutakar taimakawa wajen yaƙi da wadannan cututtukan kamar yadda Allah ya sauwake muna.

Abubuwan da za’a nema:

  • Ganyen Zogale ‘Ta Makka.
  • Ganyen Albarka.
  • Madarar gari.

Bayan an tanadi wadancan abubuwan da muka ambata sai shanya wadannan ganyayyakin a cikin inuwa inda babu rana har sai sun bushe rumus.

Idan an tabbatar sun bushe, sai yi amfani da abin daka ko niƙa sai a mayar da su gari lumui.

Yadda za’a haɗa domin amfani:

Za’a ɗebi garin Zogale, Albarka da Madara cokali ɗaya-ɗaya sai a samu ruwa masu dan zafi-zafi a kada su ciki sai a sha safe kafin a cin abinci da awa 1-2 da lokacin barci. Za’a yi hakan har tsawon kwanaki bakwai.

Bonus:

Idan akwai zuma mai kyau za’a iya haɗawa da shi domin ƙarin fa’idodi.