Illolin Amfani Da Magungunan Mata Ga Mace A Farkon Aure
Da yawa daga cikin mata musamman ma na Hausawan Afrika, musamman a Najeriya, sun duƙufa wajen amfani da wasu sinadarai don ƙara wa yayan su mata ni’ima wajen gamsar da mazajen su lokacin saduwar. To haƙiƙa, ba zai iya zama laifi in an yi irin wadannan abubuwan, amma kuma wasu matsaloli da illa da ire-iren waɗannan magungunan ke haifar wa bayan an yi amfani da su.
Zamu iya cewa illolin magungunan sun fi muhimmancin su yawa musamman ga mace mai tasowa, wato budurwa da ba ta taɓa auren farko ba.
Mata da yawa daga cikin iyaye, sun ma ɗauki wannan hanyar a matsayin sana’a ta sayar da magunguna na mata abin neman abin dogaro da kai, sukan kai tallar irin waɗannan magunguna gidajen mata musamman inda ake biki don tallata hajar su, domin samun abin sawa bakin salati.
Mafi yawancin lokuta da zarar an ce mace an sa ranar auren ta, iyaye da kuma ‘an matan da kan su, za su fara zuwa neman taimakon magungunan na sha’awa. Akan ɗauki tsawon lokaci ana haɗa mace, maimakon a bar ta ta tafiyar da kanta a kan irin tsarin da Allah Ya tsara mata da irin waɗannan magungunan da ba su da asali wanda nan gaba za’a samu rikirkicewar sha’awa domin yamutsa ta ɗin da aka yi da waɗannan sinadarai tun da farko.
Daga cikin ire-iren waɗannan sinadarai akwai da mata ke haɗawa na karin ni’ima wajen kwanciyar aure akwai:
• Na sha da madara ko a shayi.
• Na dafawa da kaji.
• Na ci da nama.
• Na ci da baru.
• Na mannawa.
Illolin da maganin ke haifar wa shine gusar da ni’imar mace na asali da take da shi kafin fara shan waɗannan magungunan:
Duk macen duniya, akwai ni’imar da Allah ya mata wajen gamsar da namiji a lokacin kwanciyar aure, amma irin ni’ima da mata ke ƙarawa kafin su yi aure na haifar masu da illa wajen gusar da ni’imar da suke da shi na asali wacce Ubangiji ya hore musu.
Domin da zarar wannan haɗin magunguna da suka yi ya gushe ko kuma ya kare aikin shi, to ni’imarta na asali da take da shi ne zai dawo saboda wancan ni’imar ƙago ta aka yi, amma kuma ba lallai ne miji ya gamsu da ita ba bayan barin magungunan. Domin wanda aka yi kafin auren da ma ba mai ɗorewa ba ne kuma zai wuce tun shan shi aka yi.
• Cire wa miji sha’awar matarsa;
Da zarar wannan haɗin magungunan da aka yiwa mace kafin ta shiga gidan mijinta ya gushe, to ni’imar ta zai ragu da kashi 80% sai na asali da take da shi ya dawo, shi kuma miji ba zai taɓa jin tana gamsar da shi kamar farkon auren su ba.
Daga nan sha’awa da yake mata zai fara raguwa, idan aka yi rashin sa’a sai ma ya haifar masa da sha’awan wasu mata a waje.
• Janyo ruwan jiki ta karfi;
Agaskiya maganin mata ban dauke shi a abu mai amfani ba,domin abune da yake janyo ruwan jiki da karfi da yaji wanda duk ranar da ruwan jikin mace ya kare tofa ta shiga uku ta lalace.
Bayan haka ga cututtuka da yake haifar wa musamman wanda mata ke turawa a cikin gaban su, ina tsammanin idan akwai ciwon sanyi to masu shi kadan ne, mafi yawan mata suna fama da ciwo ne sakamakon cushe_cushe amma sai ido ya rufe suce wai sanyi, haka nan kuma su magungunan da suka janyo wannan lalurar su ake kuma amfani dasu don neman waraka.