Lafiya

Dalilin Da Yasa Jarirai Suke Barkewa Da Kuka Idan An Haife Su

A cewar MedicalNewsToday, masu bincike sun gano cewa kukan jariri na iya dangantuwa da fitowar ruwan amniotic da ƙumburi daga huhu da kuma rashin jin daɗin haihuwa daga jin da iska mai sanyi, matsin lamba, da kuma sabon yanayi.

A cikin al’adun gargajiya, ana ganin kukan farko na jariri a matsayin shaida mai ƙarfi ta lafiyar huhu.

Jarirai suna shan ruwan amniotic yayin da suke cikin mahaifa, don haka daidaitawa da busasshiyar iskar a karon farko na iya zama mai tauri (kuma mai ban tsoro) a gare su, kuma rashin jin daɗin da suke fuskanta yayin haihuwa yana iya haifar da kuka.

Sau da yawa, jariri yana gajiya sosai kuma yana cikin ɓacin rai daga shan numfashin farko da aka haife shi har yakan yi barci kusan nan da nan.

Advertisement