Cututtukan Da Za’a Iya Magance Su Ta Hanyar Amfani Da Namijin Goro
An shafe shekaru ana amfani da namijin goro (Bitter kola) a cikin magungunan gargajiya na Afirka kuma an ce yana ba da fa’idodi da yawa na kiwon lafiya, gami da iya magance cututtukan da ƙwayoyin cuta.
Ta fannin dandano, namijin goro yana da ɗaci, da kuma ɗanɗano mai laushi. Idan aka ci namijin goro mai ɗaci yana samar da sinadirai iri-iri, waɗanda suka haɗa da carbohydrates, lipids, protein, bitamin C, calcium, potassium, iron, da caffeine, bisa ga binciken.
Amfanin namijin goro mai ɗaci sun haɗa da:
1. Maagance ciwon sanyin kashi iri-iri;- ciwon sanyin kashi da gaɓoɓi wani nau’in ciwon ƙashi ne sanya zafi ko shaka a ƙashi na rashin dadi zuwa mai tsanani. Lalacewar guringuntsi na haɗin gwiwa da ƙashin dake ciki yana haifar da ciwo mai tsanani, musamman a cikin kwatangwalo, gwiwa, da haɗin gwiwar yatsan hannu.
Masu bincike a Jami’ar Obafemi Awolowo da ke Najeriya sun yi gwajin Bitter kola kan alamun ciwon osteoarthritis, inda suka gano cewa ya rage kumburi sosai da rashin jin dadi da ke tattare da yanayin.
2. Ƙara kuzari;- namijin goro na dauke da maganin kafeyin, wanda zai iya taimakawa wajen saurin samun kuzari, musamman wajen samun saduwa iyali cikin nishadi.