Abincin Yau Da Gobe Da Ka Iya Zubarwa Mata Ciki

Pawpaw abinci ne da aka saba ci a Najeriya. Yawancin mutane suna son cin Papaya ba tare da ya nuna ba saboda ba shi da laushi sosai. A zahiri, ni a matsayina na marubuci ina son cin pawpaw wanda ba nuna ba. Kamar yadda bincike ya nuna, bai tabbatar da cewa yana da illa ga sauran mutane ba, amma lamarin ba iri ɗaya ne ba ga mata masu ciki.

Rahoton da mujallar Healthline.com ta wallafa, yace bai dace mata masu juna biyu su ci Pawpaw ba, domin Pawpaw da bai nuna ba yana dauke da Latex.

Latex wani abu ne da aka tabbatar yana haifar da kumburi a cikin mahaifa wanda ke kaiwa ga zubar ciki. Haka nan zai iya haifar da haɗari ga yaron da ke cikin ciki.

Ita dai Pawpaw da ta fito tana da wadatar ma’adanai da bitamin daban-daban, ba ta dauke da ko kadan daga sinadaran Latex, wanda hakan yasa ya zama cikakkiyar abinci ga mata masu juna biyu.