Yanda Za’a Magance Digo-Digon Baki A Fuska

Yawancin digo-digon baki da wasu ke fama da su a fuska ba su da lahani, idan mutum yana son rage fitowar su, yawancin mutane suna iya yin ta amfani da magunguna na yau da kullun, wato asibiti.

Akwai samfuran magunguna da ake sayarwa a “kemis” da yawa waɗanda zasu iya taimakawa wajen magance bakajen tambura a fuska. Wadannan magungun nan dole zama suna kunshe da sinadaren magun-guna kamar:

hydroquinone
kojic acid
retinoids
kayan aikin sinadarai
bitamin C
acid azelaic

Haka zalika, idan mun koma kan hanyoyi na gida, wato “gargajiya”, akwai muhimman magunguna da su iya warkar da ire-iren wadannan matsalolin da makamantan su.

Ba tare da bata lokaci ba, idan yanda za’a hada wannan maganin shine;

Za’a samu garin habbatus-sauda, man zaitun da ruwan khal.

Idan samu dukkan wadancan abubuwan da muka zayyana, za’a garwaya su waje daya sai a rika shafawa a inda damuwar take sau biyu rana, da safiya da kuma idan za’a shiga bacci.

Domin neman karin bayani game abinda muka bayyana a cikin wannan matsalar sai a tuntube mu akan wadannan emails; Info@arewatimes.com.ng ko uai4466@gmail.com.