Yadda Zaka Duba Idan Wani Na Bibiyar Ka A WhatsApp
Mai yuwa ana bibiyar ka duk chatting ɗinka na WhatsApp ba tare da sanin ka ba.
Tabbas hakan yana faruwa kana chats da mutane a whatsApp zata yiwu ma kana gudanar da muhimman surrikan ka na kasuwanci ko makamancin haka, wanda ba zaka buƙaci wani ya sani dukkan harkokin ba, amma wani yana nan yayi Linking ɗin whatsApp naka da wayar shi yana ganin komai da komai da kake gudanarwa na sirri.
Yadda abun yake shine, idan kana son ka tabbatar da shin ana bibiyar chats naka na WhatsApp? Insha Allahu cikin sauƙi zamu sanr daku yadda abin yake.
Mataki 1: Zaka ka buɗe whatsApp ɗin ka shiga daga cen sama wurin waɗannan Ɗigo-Ɗigo ɗin guda ukku na gefen hannun dama (Ga sunan naja masu layi a hoto) kana danna su zasu baka zaɓi kamar haka:
- New Broadcast
- Linked Device
- Starred Message
- Settings
Mataki 2: Sai ka danna “Linked Device” kana danna wannan wajen zai buɗe maka, idan har lallai ana bibiyar ka a WhatsApp, to zaka ga alamomin wayoyin ko na’urorin da suke bibiyar ka a whatsApp, zaka iya shiga ka cire su nan take domin su daina bibiyar harkokin ka, idan kuma ka gan shi kamar yadda ka gani a hoton da na saka wato sun nuna maka “Link Device” kuma a ƙasan linked device ɗin babu komai to hakan yana nuna babu mai bibiyar ka, sai dai idan kana buƙatar kayi Linking whatsApp ɗin naka da wata wayar shike nan sai kayi Linking Device ɗin.
Tabbas wannan zai taimaka wurin linking wayoyin ƙannen mu da wadanda muke da ikon kulawa da tarbiyyar su domin tabbatar da abubuwan da suke gudanarwa a manhajar WhatsApp a kowane lokaci.
Allah kai ne kaɗai kasan daidai, ka ɗora mu akan daidai a koda yaushe.