Yadda Za’a Duba Rijistar Layi Da ‘NIN’ Akan MTN, AIRTEL, 9Mobile Da GLO

Kuna neman hanyar tabbatar da idan an sami nasarar haɗa National Identification Number (NIN), ɗin ku zuwa Subscriber Identity Module (SIM) ɗin ku, to kada ku samu damuwa. A cikin wannan post zamu nuna muku hanyar yadda zaku bincika idan an sami nasarar haɗa NIN ɗinku da sim ɗinku a cikin matakai kaɗan.

Ba matsala ba ne idan har yanzu ba ku karɓi saƙon tabbacin haɗa NIN ɗin da sim din ku ba, saboda masu aiki layuka zasu iya bincika ko sun sami nasarar haɗa NIN ɗin su da lambobin wayar su kai tsaye.

Kamfanonin layuka sun bukaci masu amfani da shi da su danna *996# sannan su shigar da NIN din su domin su cigaba da amfani da layukan su.

Idan ana son gane layi da NIN sun haɗu lafiya lau, ko kuma sanin layi nawa aka haɗa da NIN din ka akan MTN, Glo, Airtel da 9Mobile, sai ka danna *996# > ka danna “4”. Bayan nan sai ka danna “2” , zaka samu sakon matsayin rajistar layin ka.