Yanda Za’a Magance Tsohon Gyambo Ta Hanyar Gargajiya
Ruwan zuma abu ne mai zaki da ɗanɗano da kudan zuma ke yi. Kudan zuma suna samar da zuma daga sigar tsiro masu zaki ko kuma daga tsirruka na wasu kwari, ta hanyar regurgitation, aikin enzymatic, da fitar ruwa.
Masu fama da tsohon gyambo ko rauni wanda ya jima yana ci muku tuwo a kwarya, to insha’Allah kun zo inda ya dace domin sanin yadda za’a magance wannan gyambon cikin sauƙi, kuma da yardar Allah a gida.
Domin maganin ire-iren waɗannan tsofaffin gymbuna da suka dade busu warke ba, ana bukatar masu fama da irin wannan matsalar da su fara samo sahihin zuma mai kyau wanda baya da wani hadi acikin shi.
Idan an samu zumar mai kyau, sai kuma a samu garin habbatus-ssauda.
Bayan an samo wannan garin, sai a kuma samo ruwan Khal.
Yadda za’a yi amfani da wadannan kayan da muka ambata shine; za’a haɗa garin habbatus-sauda da ruwan na khal a wuri daya, sai a ajiye su kamar tsawon awa ɗaya.
Bayan haka, sai a tace ruwan da abin tacewa mai tsafta.
Za’a mayar da ruwan da a aka tace a matsayin ruwan anti-bacteria da za’a rika wanke wannan gyambon a kowace rana.
Idan aka wanke wurin sosai, sai a bar shi ya dan sha iska, sannan sai a rika shafa wannan zuman a wurin. Haka za’a rika yi kowace rana, insha’Allah za’a yi muna addu’a kuma a godiya ga Allah.