Yadda Za’a Magance Tabon Ƙurajen Fuska

Matsalar kuraje da tabon fuska sun fi shafar matasa, mata da maza. Wani lokaci sai an sha wahalar magance kurajen fuska, amma sai tabo ya ki bacewa.

Rashin bacewar tabo a fuska na bata kwalliya. Sau da yawa za a ga ba a son shiga taron mutane domin wadannan tabon.

Da yawan mutane sun gwada mayukan kantin, domin rabuwa da tabon fuska. Wasu sun yi sa’a wasu kuma ba su yi sa’a ba.

A yau mun zo da bayanin yadda za a magance tabon fuska. Muna son a san cewa daya za a zaba daga cikin hanyoyin da muka lissafo, kada a hada su gaba daya. Domin yin hakan zai kara lahanta fuska ne.

• A samu ganyen dogonyaro, sai a hada shi da kurkum, sannan sai a shafa a fuska. A jira tsawon minti 15, sannan a wanke da ruwan dumi.

• Za a iya shafa markadadden dankalin Turawa a kan tabo. Hakan na magance kurajen fuska, sannan ya hana su sake fitowa.

• A daka tafarnuwa sai a shafa a kan tabo. Tafarnuwa tana wari, amma tana gyara fuska, sannan ta magance tabon fuska.

• A hada karas da tafarnuwa da zuma sai a shafa a fuska na tsawon minti 20 kafin a wanke.

• A samu hodar ‘baking soda’, sai a hada ta da ruwa, sannan a shafa a fuska zuwa minti 2 ko 3, daga nan a wanke fuska da ruwan dumi.