Yadda Za’a Duba Ragowar Data A Layin MTN

Yayin da sabbin code din *312# MTN data balance code sun shafi wasu ayyukan intanet na musamman, ana iya yin amfani da lambar code kamar wadannan *323#, sannan a danna “1” don bincika ragowar datar ku akan layin MTN a Najeriya.

Haka zalika, zaku iya duba ragowar datar hanyar message, wato SMS.

Yadda za’a duba shine, ka rubata lambar “2” ka tura zuwa “323“, nan take zaka samu sako da bayani data duka.

A karshe, har wayau zaku iya danna *323*4# kai tsaye, sai a tura 📞. Nan take zaku ga ragowar datar ku.