Yadda Za’a Busar Da iPhone In Ta Fada Ruwa Maimakon Saka Ta Shinkafa

Kamfanin kera wayoyin iPhone, Apple ya zayyana wasu hanyoyi mafi kyau domin busar da wayar iPhone idan ta fada cikin ruwa a maimakon sanya ata a cikin shinkafa idan ta fada cikin ruwa duk da shaharar da wannan wannan ta amfani da shinkafa ta yi.

Masana kayan na’urori sun dade suna gargadi game da amfani da wannan hanyar ta busar da waya a cikin shikafa domin bincike da dama sun nuna rashin amfanin wannan dabarar.

A wannan karon, kamfanin Apple ne ya fitar da bayanai da gargadi ga masu amfani da wayoyin kamfanin ƙirar iPhone cewa amfani da shinkafa domin busar da wayar da ta fada cikin na iya sanya ƙananan ƙwayoyin shinkafar su lalata wayar baki daya.

Apple ya ya bayar da shawarar cewa mutane su rika fitar da duk wani ruwa sannu a hankali ta hanyar girgiza wayar a hankali akan tafin hannu yayin da wurin cajin wayar ke kallon ƙasa, daga nan sai a ajye wayar a wuri mai iska ta bushe.

Duk da cigaban da aka samu wajen ƙera wayoyi na zamani amma har yanzu ana amfani da tsofaffin dabaru wajen gyara su idan suka lalace.

Bugu da ƙari, Apple ya yi gargaɗi game da yin amfani da abu mai zafi wajen busar da wayar, kamar amfani na’urar busar da gashi da dai makamantan su.

Kamfanin ya kuma yi gargaɗi kan cusa abubuwa kamar su auduga ko tawul ɗin takarda a cikin wayar da sunan busar da ita.

Daga karshe, ana ƙarfafa gwiwar masu amfani da iPhone da su bar wayar a wurin sanyi ko dan shi, kuma inda iska ke bugawa kafin su mayar da ita cikin caji.