Yadda Za’a Bambance Waya Mai Kyau (Original) Da Jabu

Mutane da yawa suna shiga wani yanayi a lokacin da suke buƙatar sayen wayar Android, wanda a zahirin gaskiya wayoyi sunyi tsada sosai, siyan sabuwar waya kuma sai mutum ya daure. Yana da kyau mutum jarraba wayoyin wasu kasuwanni, musamman Kano, saboda kaso mafi yawa daga wayoyin fake ne, ba original ba ne daga kamfanin waya ba.

Zai maka matukar wahala ka iya fahimtar haka ko da ka jima kana riƙe wayoyin hannu na zamani, ni dai akaran kaina na fi amfani da Samsung wajen buga-buga, kuma nafi son ta sosai. Wani lokaci zaka samu wasu Samsung ɗin ba original bane.

Da wannan muke baka shawara, indai ka tashi siyan wayar hannu ta Android, ka siya sabuwa, amma idan baka da hali, ka siya a wajen wanda ka sani. Idan kuma har ta kai ka ga siya a kasuwar tsofaffin waya, zan baka wannan hanya ɗin don gane waya mai kyau (original) ce, ko jabu (fake):

  1. Idan aka baka waya, ka shiga wajen inda ake saka kati, ka rubuta *#06#
  2. Numbobin wayar mai suna IMEI zasu fito, guda 15 a sama, guda 15 a ƙasa. Ko na saman, ko na ƙasan, sai ka ɗauke su, ka shiga wannan shafin yanar gizo ɗin
    https://imeicheck.com
  3. Kana shiga, sai ka je in da aka rubuta “Check IMEI for Free” sai ka je kayi pasting ko ka rubuta IMEI ɗin da wayar ta nuna guda 15 ɗin nan.
  4. In dai waya original ce, duk wani information nata zai fito na gaskiyar, ciki har da garin da aka yi ta. Idan kuma ba daga wannan kamfanin take ba, za’a ce maka ba’a san da wayar ba.

Muna zamanin da a yanzu anan Najeriya ana iya buga wannan IMEI ɗin, idan ka siya waya wacce ba ainihin ta kamfanin ba, shine kana yin updating software version ɗin ta, ko factory reset, sai ta yi sizin ko thumbprint ɗin ta daina aiki, sauran su, da IMEI, da abubuwa makamantan haka. Wata wayar kuma bama zata yi maka wasu abubuwan ba, ka rasa dalili sama ko kasa.