Yanda Za Ka Dubi Data Balance Akan Layin GLO

Danna *127*0# akan wayar ka. Bayan dannan wadannan lambobin da tura su, za ku sami rubutu ko sakon SMS wanda ke nuna ragowar datar ku ta GLO.

Ko kuma ku danna *777# domin sayen data da sauran zabubbuka akan aikin intanet na GLO.

Amma kuma, hukumar sadarwa ta NCC ta umarci kamfanonin sadarwa a Najeriya sauya gajerun lambobin saka kati, binciken kudi da sayen Data zuwa na bai ɗaya.

Domin saye ko duba Data da sauran su, kuyi amfani da dannan lambobin; “312# ko duba data *323#.