Yadda Ake Yin P2P Verification Na Sidra

Matakai don nasarar aikin tabbatar da P2P ba tare da damuwa ba zai kasance kamar yadda zamu bayyana a matakan da ke ƙasa:

1: Shiga asusu ka ko Application na Sidra.

2: Danna WALLET.

3: Danna aika (send).

4: Rubuta sunan mai amfani da Sidra ko username, misali (usil).

5: danna search bayan rubuta suna ko username, sai mutum ya bayyana.

6: Danna hoton wanda kayi searching. Zai kai ka profile din shi.

7: Sai a danna P2P.

8: Daga nan sai a danna (Request Verify).

9: Ka fadawa wa mutumin ya shiga account din shi na Sidra ya karba ta hanyar danna profile din shi. Zai kai shi a shafin Kycport.p2p, daga zai gan ka a can sai ya karɓa.

10: Bayan mutum ya karba, takardun kyc din shi zai bayyana akan wayar ka. Sai ka danna daukar bidiyo.

11: Mutum zai rike rike (daftarin) da yayi amfani da shi a lokacin KYC, misali (NIN ko Passport), sannan a yi bidiyon shi/ta. Bidiyon zai tsaya kai tsaye da kan shi bayan wasu dakikoki, sannan gangara ƙasa domin danna (Submit).