Xiaomi Ya Kirkiri Kare Na “Robot” Domin Tsaro

Xiaomi ya gabatar da kare na “robot” wanda akae kira (CyberDog 2) a taron Duniya na Wayar hannu, wani karwn na’urori mai rubu’in halitta wanda ke nuna yanayin hadewa da tsarin yanke shawara ta hanyar firikwensin 19.

Wato karen zai iya yin ayyukan da kan shi da na’urorin ji da shin-shina dake haɗe da shi.

An ƙera shi don tsaro, robot ɗin yana nuna sadaukarwar Xiaomi don haɓaka aikin kirkira. Tare da fasaha mara iyaka, masu haɓakawa na iya tsara ayyukan karen, kuma yana da nauyin 40% ƙasa da wanda ya gabace shi, wato CyberDog 1.

An CyberDog 2 yana dauke da micromotors 12 da dandamali na ƙarfafa AI, yana nufin ci gaba da haɓaka fasaha.

An saka farashin CyberDog 2 a $3,000, kimanin fiye da miliyan uku da rabi (N3,500,000) kudin Najeriya. CyberDog 2 yana da ƙarfi ta hanyar na’urar NX, tana ba shi damar kewaya mahalli ba tare da wahala ba, yana nuna babban tsalle a cikin robots.