Wene Ne Masallacin Qudus

Wannan masallacin na biyu da kuke gani na biyu a cikin wadannan hotuna shi ne Masallacin Qudus (Al Aqsa) ba wannan na farko ba da yake ɗauke da kalar zinare a saman shi, wancan ɗin sunan shi Dome Of The Rock.

A lokuta da yawa, mutane da dama na samun ruɗani akan Masallacin Qudus da kuma wurin da ake kira (Dome of the Rock) da ke kasar Falasɗinu, wanda Musulmi da Yahudawa da Kirista suke zuwa suna bauta a wurin.

Duk da yake dukkan su sun kasance gine-gine guda biyu daban-daban masu tsarki a wuri ɗaya.

Masallacin Qudus dai shi ne wuri mafi daukar hankali a Duniya saboda MUSULMI da YAHUDAWA da KIRISTA sun ɗauke shi wuri mai tsarki duba da dangantakar shi da abubuwan da suka faru na tarihi a rayuwar Annabawan Allah da suka rayu a wannan wuri mai daraja.