Lafiya

Dalilan Da Ke Kawo Rashin Karfin Azzakari Ga Maza

Karfin azzakari ya dogara ga abubuwa da yawa da suka haɗa da shekaru, lafiyar gaba ɗaya, matakan hormone, jijiyoyi, kwararar jini, yanayin tunani, da motsin rai.

Lokacin da kowane ɗayan waɗannan abubuwan ya samu wata tangarɗa, matsalar rashin ƙarfin azzakari na iya faruwa.

Yiwuwar rashin karfin mazakuta yana karuwa da shekaru, duk da haka, ba shekaru ba ne kadai ke haifar da raunin karfin azzakari ba. Wasu dalilai da yanayi kuma na iya haifar da tabarbarewar mazakuta. Waɗannan abubuwan sun haɗa da:

Damuwa: Jima’i yana buƙatar tunani da jiki suyi aiki tare. Ayyuka da gajiya kamar matsaloli a wurin aiki, matsalolin dangantaka ko damuwar kuɗi na iya haifar da rashin ƙarfin azzakari.

Yanayin Lafiya: Sau da yawa rashin karfin azzakari yana da alaƙa da matsalolin rashin lafiya da kuma yanayin da ke shafar kwararar jini a cikin al’aura, kamar su ciwon sukari, hawan cholesterol, hawan jini, kiba, cututtukan zuciya, sclerosis mai yawa, da cutar Peyronie.

Rauni: Raunuka zasu Iya haifar matsalar rashin karfin azzakari. Misali rauni wanda ya shafi lakar gadon baya wanda ka iya lalata jiyojin dake saka azzalari ya miƙe.

Daukar dogon lokaci ana tuka keke shima yana iya hana jini zagayawa, sai ya haifar rashin karfin azzakari. Hazalika wasu magungunan kashe zafin ciwo da ake baiwa maza masu rauni ka iya kawo wannan matsalar.