Tarihi

Wane Ne Paul-Henri Damiba, Jagoran Juyin Mulkin Burkina Faso?

Wani Laftanar Kanal da aka nada domin kula da harkokin tsaro a babban birnin Burkina Faso ya zama jagoran juyin mulkin da sojoji suka hambarar da gwamnatin shugaba Roch Kabore bayan an yi ta harbe-harbe a Ouagadougou.

Sanye da kayan soji da jajayen kaya, an gabatar da Paul-Henri Sandaogo Damiba a matsayin shugaban kungiyar Patriotic Movement for Safeguard and Restoration (MPSR), wacce ta kwace mulki ranar Litinin.

“MPSR, wanda ya hada da dukkan sassan sojojin kasar, ya yanke shawarar kawo karshen mukamin shugaba Kabore a yau,” in ji wani kaftin da ke tsaye a gefen hagu na Damiba, yayin da yake karanta wata sanarwa a cikin sunan Laftanar Kanar a gidan talabijin na Radiodiffusion na Burkina (RTB).

A watan Disamba ne Kabore ya karawa jami’in dan shekaru 41 karin girma zuwa kwamandan yankin soja na uku na Burkina Faso, abin da wasu manazarta ke kallo a matsayin kokarin da shugaban kasar ya yi na samar da goyon baya a cikin sojojin.

Nadin ya biyo bayan harin da mayakan suka kai a wani sansanin Jandarma a garin Inata na arewacin kasar wanda ya kashe jami’an soji 49 da fararen hula hudu.

Rahotannin da ke cewa sojojin sun shafe makonni biyu ba tare da wani abinci ba, ya haifar da zanga-zangar kin jinin gwamnati da kuma kira ga Kabore ya sauka daga mulki.

A sabon mukamin nasa, Damiba ya ci gaba da sake fasalin aikin soja, inda ya nada sabbin hafsoshi a wasu muhimman mukamai da nufin yakar masu tayar da kayar baya.

Sabanin Kabore, wanda sojoji ke zargi da tashe-tashen hankulan ‘yan tawaye, Damiba ya nemi ya bayyana kansa a matsayin kwararre kan yaki da ta’addanci.

Ya yi karatu a wata makarantar soji da ke birnin Paris, inda ya sami digiri na biyu a fannin kimiyyar laifuka daga Conservatoire National des Arts et Metiers.

A watan Yuni, ya buga wani littafi mai suna Sojojin Yammacin Afirka da Ta’addanci: Martani mara tabbas? inda ya yi nazari kan dabarun yaki da ta’addanci a yankin Sahel da iyakokinsu.

Daga 1987 zuwa 2011, yana cikin Regiment na Tsaron Shugaban Kasa (RPS) na tsohon shugaban kasar Blaise Compaore, wanda aka hambarar a a shekarar 2014 bayan daruruwan dubban mutane suka fantsama kan tituna domin nuna adawa da shirin tsawaita mulkinsa.

Daga nan sai gwamnatin rikon kwarya ta rusa rundunar, lamarin da ya janyo bacin rai a tsakanin wasu jami’an.