Wane Ne Nasir I. Mahuta?

Nasir I. Mahuta ɗalibin Ilimi ne ma’abocin bincike da nazari a fannonin ilimi da dama, musamman ilimin daya shafi fasahar zamani (Technology).

Kwararren Software Developer ne mamallakin Kamfanin Sa’a Ltd .

Kwararren dan kasuwar Internet ne (Digital marketing), mai shaidar kwarewa ta Kamfanin Google.

Dalibin fasahar Blockchain ne da ke da shaidar kammala gajeren karatun “The Blockchain ‘ a University Of California, Irvine.

Dalibin Cryptocurrency ne dake da shaidar kammala karatun Diploma akan Cryptocurrency a Alison. Bugu da Kari; ya kuma horar da matasan fiye da 3000 kasuwancin Crypto, sannan kwararren mai bada shawara Ne akan kasuwancin Crypto.

Nasir I. Mahuta shine mamallakin littafin nan da har yanzu ba’a samu irin sa ba, wato sirrin Crypto, muna rokon Allah ya jikan Malami Nasir I. Mahuta da rahamar sa, Allah yasa ya huta.

Amin